My Authors
Read all threads
1. MA'ANAR KABBARA: Kabbara na nufin jinjina da yabo ga Allah madaukakin sarki, tare da nuna Girman sa, da tsarkake shi daga nakasa ko tarayya a gurin bauta. Allah madaukakin sarki yana cewa: "ولتكبروا الله على ما هداكم" a wata ayar yana cewa: "وربك فكبر".
2. Ita kabbara ana yinta ne a kowani lokaci da musulmi ya samu sararin yinta, musamman a cikin kiran sallah, ko a cikin sallar da kanta, ko kuma a yayin da musulmi yaga wani abin mamaki, da makamantan haka.
3. Amma a lokacin Idi (guda biyu), an fi son musulmi ya yawaita kabbara a duk halin da ya sami kansa, an karbo daga Abdullahi dan umar yace a hakkin manzon Allah SAW:
"كبر في عيد ثنتي عشرة تكبيرة، سبعا في الأولى وخمسا في الآخرة، ولم يصل قبلها ولا بعدها".
4. KABBARAR IDI: a nan zamu iya kasa kabbarar idi guda biyu:
A. Kabbara sakakka (مطلقة): ita wannan kabbarar ba ta da wani lokaci da aka kebance ta da shi, wato musulmi ze iya yinta a duk lokacin da ya samu sarari, a gida yake, ko kasuwa, ko masallaci, ko ma ina ne ze iya yinta.
5. A sallar idi karama: ita wannan kabbarar a sallar idi karma ana fara ta ne daga lokacin da rana ya fadi (dab da sallar magariba) na ranar karshe na watan azumi (dai dai yake anyi azumi ashirin da tara ne ko talatin),
6. sannan ana gamata ne lokacin da liman ya gama hudubar sa na sallan Idi.
7. Shiyasa Allah yake cewa:
"ولتكملوا العدة ولتكبروا الله على ما هداكم ولعلكم تشكرون".
8. A sallar idi babba: kabbara sakakka (wacce akeyinta a kowani lokaci) ana fara yinta ne daga ranar farko na Zulhijja har zuwa rana na goma sha uku na zulhijja.
9. Akan haka Allah yake cewa:
"ليشهدوا منافع لهم ويذكروا إسم الله في أيام معلومات".
10. Duk da cewa yawancin malumma sun tafi akan cewa "أيام المعلومات" sune kwana goman farko, akan haka ne Abdullahi dan Abbass ya tafi, kuma ya kafa hujja da hadisin annabi da yake cewa:
11. "ما من أيام أعظم عند الله ولا أحب إليه من العمل فيهن من هذه الأيام العشر، فأكثروا فيهن من التهليل، والتكبير، والتحميد".
12. "Babu wasu kwanaki da suka fi girma a gurin Allah, kuma ayyuka suka fi soyuwa a cikin su fiye da wannan kwanaki guda goman, ku yawaita ambaton Allah, da kabbara, da godiya (a cikin su)".
13. Wannan hadisin na nuna mana falalar wannan kwanaki guda goman na zulhijja, kumma annabi SAW ya umarce mu da yawaita fadan (LAILAHA ILLA LAHU, ALLAHU AKBAR, ALHAMDULILLAH) a cikin su.
14. Amma duk da haka wasu malumman sun kara kwana uku na bayan sallah ("أيام النحر"التشريق) a cikin kwanakin da Allah ya ambata da "أيام معلومات".
15.
B. Kabbara da aka tsarketa (المقيدة): wannan itace kabbarar da ake yinta bayan salloli guda biyar (wasu malumman sunce har da sallolin nafila).

malumma sun samu sabani akan hukuncin ta kamar haka:
16. I. AHNAF: Ahnaf sun tafi akan cewa wannan kabbarar wajiba ce so daya, idan mutum yayi kari babu laifi, suka kara da cewa ana yin kabbaran ne a salloli guda takwas, farawa daga sallar asuba ta ranar jajibi (Arafa), zuwa la'asar ta ranar sallah.
17. Wasu daga cikin su kuma sunce ana yin ta ne bayyan salloli guda goma sha uku, farawa daga sallar asuba ta ranar Arafa zuwa la'asar ta rana ta hudu (wato rana ta uku bayan sallah).
18. Sigar kabbara a gurin su:
الله أكبر الله أكبر، لا إله إلا الله والله أكبر، الله أكبر ولله الحمد".
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LAILAHA ILLAL LAHU WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR WA LILLAHIL HAMD. (Haka sayyidina umar yakeyi, da Abdullahi dan mas'ud da thauri).
19. II. MALIKIYYA: Mazhabar malikiyya suna ganin yin kabbara bayan salloli lokacin idi sunnah ce akan musulmi, kuma ana farata ne daga sallar Azahar ta ranar Idi, zuwa asuba ta rana ta hudu bayan sallah (wato salloli Ashirin kenan).
Wannan ita aka fi yi a bangaren West Africa.
20. sigar kabbara a gurin malikiyya: malikiyya na da siga guda biyu zuwa uku, kamar haka:
١. الله أكبر، الله أكبر".
٢. "الله أكبر، الله أكبر، لا إله إلا الله، والله أكبر، الله أكبر، الله أكبر، ولله الحمد"
21.
1. ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR.
2. ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAH, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD.
3. (wasun su sunce a kabbara ta farko mutum ze iya maimaita ta so uku: Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar).
22. III. SHAFI'IYYA: Shafi'awa suna da magana biyu ko uku akan hukuncin kabbara lokacin idi, wanda daya daga ciki sun tafi akan irin maganar malikiya.
Amma wanda yafi yaduwa a gurin su shine musulmi zeyi kabbara bayan sallar farilla da nafila a lokacin Idi.
23.

sigar kabbara a gurin su:
"الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر، لا إله إلا الله، والله أكبر، الله أكبر، ولله الحمد، الله أكبر كبيراً، والحمد لله كثيراً، وسبحان الله بكرة وأصيلاً، لا إله إلا الله وحده، صدق وعده، ونصر عبده، وأعز جُنده، وهزم الأحزاب وحده"
24.
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAH, WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD, ALLAHU AKBAR KABIRA, WAL HAMDULILLAHI KATHEERA, WA SUBHANALLAHI BUKRATAN WA ASILA,
25.
LAILAHA ILLAL LAHU WAHDA, SADAQA WA'ADAH, WA NASARA ABDAH, WA A'AZA JUNDAH, WA HAZAMAL AHZABA WAHDAH.
26.
IV. HANABILA: Hanbaliyya sunce kabbarar ana yinta ne a cikin jama'a, limami ze fuskanci jama'a yana yi suna amsawa. Kuma zeyu mutum yayi kabbarar so daya kawai ya wadatar.
27.
sigar kabbara a gurin su:
الله أكبر، الله أكبر، لا إله إلا الله، والله أكبر، الله أكبر، ولله الحمد".
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD.
28. Wannan shine sabanin da aka samu a gurin malumma, na yanda akeyin kabbara, da lokacin yinsa, kuma ko wanne daga cikin su ya dogare ne da hadisan manzon Allah ingantantu, shiyasa idan kaga dan uwanka yayi sabanin abinda ka aikata, bashi yake nuna cewa beyi daidai ba.
29. Annabi yanacewa: "اختلاف أمتي رحمة" sabanin Al'umata rahma ce.

BARKA DA SALLAH.
30.

Thank you for reading.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah.
Abdullahi Muaz Raihan
29/7/2020
Missing some Tweet in this thread? You can try to force a refresh.

Keep Current with DKF Raihan (ريحان)

Profile picture

Stay in touch and get notified when new unrolls are available from this author!

Read all threads

This Thread may be Removed Anytime!

Twitter may remove this content at anytime, convert it as a PDF, save and print for later use!

Try unrolling a thread yourself!

how to unroll video

1) Follow Thread Reader App on Twitter so you can easily mention us!

2) Go to a Twitter thread (series of Tweets by the same owner) and mention us with a keyword "unroll" @threadreaderapp unroll

You can practice here first or read more on our help page!

Follow Us on Twitter!

Did Thread Reader help you today?

Support us! We are indie developers!


This site is made by just two indie developers on a laptop doing marketing, support and development! Read more about the story.

Become a Premium Member ($3.00/month or $30.00/year) and get exclusive features!

Become Premium

Too expensive? Make a small donation by buying us coffee ($5) or help with server cost ($10)

Donate via Paypal Become our Patreon

Thank you for your support!